Hukumomin lafiya na Najeriya zasu karbi riga kafin korona miliyan 41

0 76

Hukumomin lafiya na Najeriya sun ce suna daf da karbar riga kafin korona miliyan 41 a zuwa karshen Satumba.


“Mun samu bayanin cewa karkashin tsarin Covax za a aiko mana da alluran cikin watannin nan masu zuwa. Allurai 3,924,000 daga Oxford/AstraZeneca Moder na zuwa karshen Yuli ko farkon Agusta 2021,” a cewar Shugaban hukumar ci gaban kiwon lafiya a matakin farko, Faisal Shuaib.


Ya kuma ce sama da alluran Pfizer da Moderna miliyan shidda za su samu daga tsarin na Covax a Agusta da allurai miliyan 29 daga Johnson and Johnson a watan Satumba kamar yadda BBCHausa suka ruwaito.


Har ila yau kawo yanzu kasar Najeriya ta yi wa sama da mutum miliyan uku allurar riga kafin tun daga watan Maris zuwa yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: