A kalla mutum 30 ne jami’an hukumar EFCC ta Najeriya suka kama a yayin wani samame a Otel din Parktonian a unguwar Lekki ta jihar Legas dake kudancin kasar.

A lokacin samamen na ranar Talata, jami’an EFCC sun samu shiga dakunan wadanda ake zargin ne ta hanyar kwace makullan dakunansu daga jami’an otel din da karfin tsiya kamar yadda majiyar mu ta fitar.

wata jarida ta ruwaito cewa EFCC ta bayyana cewa an kama mutanen ne bisa zargin aikata zamba ta intanet.

EFCC ta ce ta samu bayanan siri da suka tabbatar mata da cewa otel din ya zama matattarar masu aikata zamba da yaudara ta intanet, shi ya sa ta aika jami’anta domin gani da idon su.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: