Majalisar wakila ta Najeriya ta bukaci gwamnatin Najeriya data yi watsi da matakin bai wa jami’an kashe wuta bindiga (kwana-kwana).
A baya gwamnati ta sanar da shirinta na mika wa majalisar dokoki kudirin yi wa dokar ‘yan kwana-kwana garambawul ta hanyar bai wa jami’an damar rike makamai don kare kansu daga hare-haren da ake kai masu a yayin gudanar da ayyukansu.
Sai dai majalisar ta bukaci gwamnatin ta dakatar da matakin.
Kamar yadda BBCHausa ta ruwato a rahotan ta, Honarabul Thomas Ereyitomi wanda ya gabatar da bukatar a gaban majalisar ya bayyana cewa hukumar ‘yan kwana-kwana hukuma ce ta farar hula ba ta tsaro ba.
Sannan ya ce hankali ma ba zai dauka ba idan aka ba su damar rike bindiga saboda ba sa bukatarta.