Gwamna Badaru Abubakar ya karbi takardar Izinin kafa Jami’ar Fasaha ta gawamnatin tarayya a garin Babura

0 86

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar, ya karbi takardar Izinin kafa Jami’ar Fasaha ta gawamnatin tarayya a garin Babura a hannun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Babban Mataimakin Gwamna kan Sabbin Kafafen Sadarwa na Zamani Auwal Danladi Sankara, wanda aka rabawa manema labarai, inda ya kara da cewa za’a gina Jami’ar ne a Babura.

Sanarwar ta ce Gwamna Badaru Abubakar, ya godewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa amincewa da gina Jami’ar a jihar Jigawa kuma a karamar hukumarsa ta Babura.

Haka kuma Gwamna Badaru, ya godewa Shugaba Buhari bisa ware Naira Biliyan 4 domin fara ginin Jami’ar Fasahar a Babura, wanda hakan ya nuna irin Namijin kokarin Shugaba Buhari ta fuskar habaka Ilimi.

Kazalika, Sanarwa ta ce Gwamna Badaru ya karbi Lasisin ne daga hannun Ministan Ilimi na Kasa Malam Adamu Adamu tare da gode masa bisa amincewa da ginin Jami’ar a Babura.

Leave a Reply

%d bloggers like this: