‘Yan sanda a jihar Jigawa sun kashe wani shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane mai suna Abdullahi Bummi.

An kashe shugaban ‘yan bindigan ne a wani samame kan inda suke boyewa a Gallu, karamar hukumar Yankwashi a jihar.

Haka kuma ‘yan sanda sun ceto wata mata mai shekara 65 a samamen da aka gudanar a wani aikin hadin gwiwa na tsakanin rundunonin ‘yan sanda na jihar Katsina da Jigawa.

Jami’in hulda da jama’a na jihar Katsina, SP Gambo Isah ya shaida wa manema labarai cewa an sace matar da aka ceto ce, mai suna Hajiya Hasana Zubairu ran 29 ga watan Yunin wannan shekarar a karamae hukumar Sandamu ta jihar Katsina.

Wannan rahoton BBCHausa ne da suka ruwaito.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: