Sama da mutane 42 sun hallaka a wata gagarimar ambaliya

0 70

Akalla mutane sama da 42 sun hallaka a yammacin kasar Jamus ya yin da ambliyar ruwa da ba a taba ganin irinta ba ta afkawa wasu sassan kasar.

Haka kuma mutane da dama sun bata.

Iftila’in ya fi shafar jihohin North Rhine da Westphali da Rhineland da kuma Palestine bayan da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya, abinda kuma ya sa bakin koguna suka balle.

Ambaliyar ruwan ta lalata gidaje da gadoji da kuma hanyoyi.

Akalla wasu mutane 6 sun mutu a makociyar kasar ta Belgium kuma hukumomi sun bukaci dukkan mazauna birnin Liege da su fice.

Lamarin ya shafi kasar Holland sosai inda kogunan dake ambaliyar ruwa suka lalata gidaje da dama kuma an kwashe mutane a gidajen raino da dama.

Shugabar Jamus, Angela Merkel, wacce take kasar Amurka domin ganawa da shugaba Joe Biden, tace ta kadu matuka dangane da iftila’in.

Leave a Reply

%d bloggers like this: