Aƙalla mutum 17 sun mutu sakamakon zaftarewar kasa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

0 213

A wani labarin kuma, aƙalla mutum 17 sun mutu sakamakon zaftarewar kasa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Bala’in ya afku ne da daddare ranar Lahadi a kusa da gabar kogin Kongo, a arewacin birnin Lisala, babban birnin lardin Mongala.

Mata bakwai da maza bakwai da yara uku ‘yan kasa da shekara biyar ne suka mutu.

An yi jana’izar su a ranar da abin ya faru saboda rashin wurin ajiye su a dakin ajiyar gawarwaki na yankin kamar yadda jami’in Lisala, Désiré Koyo ya shaida wa BBC.

Mutuwar ta biyo bayan mamakon ruwan sama da aka kwashe kwanaki ana yi.

Shaidu sun ce gidaje da dama da ke kusa da kogin sun nutse kuma mazauna yankin na ƙoƙarin aikin ceton mutane daga baraguzan ginin.

Gwamnan Mongala, César Limbaya, ya aika da ta’aziyya ga dukkan iyalan waɗanda suka mutu. Ya kuma ayyana kwanaki uku na zaman makoki tun daga ranar Litinin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: