A kalla mutane 3 ne suka mutu biyo bayan rusawar wani gini a kan su a kyauyen Yakasawa-Kwari na karamar hukumar Ringim ta Jihar Jigawa.

Kakakin Rundunar Yan sandan Jihar Jigawa ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Duste.

A cewarsa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 5:00 na Safe sakamakon mamakon ruwan sama.

ASP Lawan Shiisu Adam, ya ce yan sanda sun sami rahoton wani mutum mai suna Garba Lawan mai shekaru 48, cewa Daki ya fado a kan Yayansa 3 da suke barci a cikinsa.

Sanarwar ta ce da taimakon yan sanda da kuma mutanen Garin Yakasawa Kwari, an fitar da baraguzan ginin, inda aka garzaya da Yaran zuwa Babban Asibitin Ringim.

Haka kuma ya ce likitoci sun tabbatar da mutuwar Yaran.

Kwamishinan yan sanda na Jihar Jigawa CP Aliyu Sale Tafida, ya gargadi mutanen jihar nan su kasance masu yin taka tsantan akan gine-ginen su.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: