Ministan Lafiya na Kasa ya bukaci Likitoci masu neman kwarewa su janye yajin aikin da suke yi

0 242

Ministan Lafiya na Kasa Dr Osagie Ehanire, ya bukaci Likitoci masu neman kwarewa su janye yajin aikin da suke yi a yanzu haka.

A ranar 1 ga watan Agustan da ya gabata ne Kungiyar Likitoci Masu Neman suka shiga yajin aiki, biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan su Albashin su da kuma wasu hakkokin su.

Duk irin kokarin da Masu Ruwa da tsaki a fannin lafiya da yan majalisar wakilai da kuma gwamnatin tarayya suka yi domin janye yajin aikin amma abin ya ci tura.

Da yake yiwa manema labarai jawabi a taron kwamatin yaki da cutar corona Mista Ehanire, ya bukaci likitocin su janye yajin aikin da suke yi, inda ya ce gwamnatin tarayya zata biya dukkan hakkokin likitocin.

A cewarsa, a satin da ya gabata ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da Kungiyar Kwararrun Likitoci ta Kasa, inda ya umarci sufito da hanya mai sauki domin sulhuntawa, ba tare da jefa rayukan yan Najeriya cikin hadari ba.

Ministan ya ce gwamnatin shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta biya Basussukan da ta gada daga gwamnatin baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: