Gwamnatin Tarayya ta cire kasar India daga cikin kasashen da ta hana su shigowa Najeriya saboda karuwar yaduwar cutar Corona a kasar.

A watan Mayun da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta hana matafiya daga kasashen Brazil da India da Turkiya shigowa kasar nan.

Da yake jawabi a taron kwamatin shugaban kasa kan yaki da cutar corona, inda suke yiwa manema labarai karin haske, Sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha Gida ya ce an samu cigaba sosai kan dakile cutar a Nahiyar Asia.

Boss Mustapha, ya ce kwamatin sa, zai samar da wani tsari mai dorewa kan cire kasar a kwanan nan, inda ya kara da cewa lamura kan cutar suna cigaba da dai-daita.

Haka kuma ya ce gwamnatin tarayya tana kokarin kakaba wani tsari domin yiwa ma’aikata rigakafin cutar corona a wuraren ayyukan su da kuma gidajen su.

Kazalika, shugaban Kwamatin ya shawarci yan Najeriya su rika daukar katin shaidar anyi musu rigakafin cutar corona a duk lokacin da zasu bar kasar nan domin tabbatarwa kasashen da suke je cewa an yi musu rigakafin a nan Najeriya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: