Adadin mutanen da Cutar Kwalara ta hallaka a jihohi 22 da suke fadin kasarnan ya kai 1178

0 108

Adadin mutanen da Cutar Kwalara ta hallaka a jihohi 22 da suke fadin kasarnan ya kai dubu 1,178, a cewar Cibiyar Dakile yaduware cututtuka ta Kasa NCDC.

Shugaban Hukumar ta NCDC Dr Chikwe Ihekweazu, shine ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a jiya.

A ranar 9 ga watan Agusta, Cibiyar NCDC ta rawaito cewa kimanin mutane 816 ne suka a jihohi 22 da suke fadin kasarnan ciki harda babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban hukumar ya ce rahoton da suka tattara na ranar 14 ga watan Agusta kimanin mutane dubu 37,819 ne suka harbu da cutar ta Kwalara.

A cewarsa, an samu mutanan ne a Jihohin Benue, Delta, Zamfara, Gombe, Bayelsa, Kogi and Sokoto.

Sauran Jihohin sune Bauchi, Kano, Kaduna, Plateau, Kebbi, Cross River, Niger, Nasarawa, Jigawa, Yobe, Kwara, Enugu, Adamawa, Katsina, Borno, Taraba da kuma birnin tarayya Abuja.

Haka kuma ya shawarci mutanen Jihohin su kasance masu tsabtace Jinkunan su, da muhallansu domin dakile yaduwar cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: