Shugaba Joe Biden ya ce ba zai sauya matakin da ya dauka na janye dakarun Amurka daga kasar Afghanistan ba

0 97

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ba zai sauya matakin da ya dauka na janye dakarun Amurka daga kasar Afghanistan ba duk da sukar da ake yi wa gwamnatinsa.

Ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi ga ‘yan kasar kai-tsaye ta gidan talabijin.

Shugaba Biden ya ce ba zai sauya matakin da ya dauka ba.

Ya kara da cewa a ko da yaushe yana yi wa Amurkawa alkawarin cewa ba zai boye musu komai ba, amma ya kara da cewa yadda ‘yan Taliban suka yi gaggawar kwace ikon Afghanistan ya faru cikin sauri.

Ya kara da cewa ya shaida wa ‘yan Taliban cewa ma’aikatansa za su ci gaba da zama a kasar kuma idan wani mummunan abu ya same su, to kungiyar za ta dandana kudarta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: