Akalla Mutane 46 aka Kashe a Kauyen Umogidi Dake Jihar Benue

0 63

Akalla mutane 46 aka bada rahotan an kashe a kauyen Umogidi dake karamar hukumar Otukpo a jihar Benue.
kazalika yan ta’adda sun mamaye wani kauye a karamar hukumar inda suka kashe mutane 3.
Shugaban karamar hukumar Otukpo Bako Eje, wanda aka kashe dan sa a harin, ya fadawa manema labarai cewa yan bindiga sun mamaye kauyen a jiya laraba inda suka shafe awanni 24 suna harbin kan mai uwa da wabi.
Bako Eje, yace da safiyar yau kimanin gawarwaki 46 suka gano yayinda mutane da yawa suka bace.
Shugaban karamar hukumar yace dan na sa da wasu yan uwan sa uku harin na jiya laraba ya rutsa da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: