Akalla wasu mutum 11 ne aka bayyana cewa an bindige su har lahira a jihar Katsina

0 63

Akalla wasu yan kauyen Dan Kumeji 11 ne aka bayyana cewa an bindige su har lahira, a kauyen dake yankin karamar hukumar kankara ta jihar Katsina.

An bayyana cewa wasu mutane 6 da suka tsallaeke Rijiya da baya yanzu haka suna karbar magani a asibiti.

Wani mazaunin kauyen mai suna Abdulmumini Sani wanda ya tabbbatar da faruwar lamarin a wata hira da akayi da shi ta wayar tarho, yace yan bindigar sun farwa kauyen ne da misalin karfe 11 na daren jiya alhamis, inda suka fara Harbin kan mai uwa da wabi.

Ya kara da cewa, a safiyar yau juma’a sun tsinci gawarwakin mutane 11 da aka kashe su bayan kai wannan mummunan harin,  tare da tabbatar da cewa sun kammala shirye shiryen su wajan fara binne mamatan kamar yanda addinin musulunci ya tanada.

Anasa bangaren kakakin rundunar yansadan jihar SP Gambo Isah kawo yanzu bai tabbatar da faruwar lamarin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: