“Mun fara sanya yayanmu a makarantun koyon sana’a”, a cewar iyaye mazauna jihar Kaduna

0 80

Matsanancin rashin tsaron da ake fuskantar a kasar nan, ya sanya wasu iyaye a jihar Kaduna yanke hukuncin sanya yayansu a makarantun koyon sana’a, saboda rashin sanin takamamman  lokacin dawowa makaratu bayan kulle su na dindin.

Kafin hakan dai Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya bayar da rahotan cewa, gwamantin jihar Kaduna a ranar 6 ga watan Agustan nan, ta yanke hukuncin rufe makarantun jihar na sai babata ta gani, biyo bayan shawarwarin da hukumomin tsaron jihar suka basu.

A cewar gwamantin sun yanke wannann hukuncin ne da izinin iyayen dalibai da kuma kuma su daliban domin kare lafiyar su, biyo bayan hare hare daga yan bindiga da satar mutane domin neman kudin fansa.

Wani mahaifi mai suna Ibrahim Yusuf wanda yayansa dalibai ne a wasu makarantu a jihar, ya bayyana cewa lafiyar Yayansa tafi komai sannan ya bukaci gwamnatin jihar da tayi amfani da kafafen yada labarai kamar su RADIO, da gidan Tv da kuma kafafen sandarwa na zamani wajan ci gaba da koyar da dalibai daga gida.

Anasa bangaren wani mazaunin jihar kaduna mai suna Abel Steben ya bayyana cewa, yana koyarda Yayansa daga misalin karfe 4 na yamma bayan ya dawo daga wurin aikinsa. Haka kuma ya bukaci sauran iyaye akan kada su bar yayansu suna wasa, amaimaikon haka gwara suke koyarda dasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: