An gano hanyar da za a rage kamuwa da cutar Maleria da ke fuskantar kananan yara a Nahiyyar Afrika
Wani binciken kwararru na kwananan da kaa gudanar ya bayyana cewa ansamo hanyar da zai rage kamuwa da cutar Maleria da ke fuskantar ga kananan yara a nahiyyar afrika da kashi 70 cikin 100.
A cewar manazartan birnin Landan dake kasar Amurka, bawa yara kanana maganin cutar zazzaban cizon sauro zairage yawan kamuwa da cutar a fadin nahiyyar afrika.
Haka kuma an gwada maganin a kasar Burkina faso, wanda aka bawa yara yan kasa da watanni 17 sun dubu 6 da suka warke daga zazabin.
Haka kuma rahoton baya bayan da aka fitar angano cewa a kowacce shekara a nahiyyar afrika ana samun mutuwar akallla yara dubu 400 kowacce shekara.
Zazzabin cizon sauri na daya daga cikin mayan cututuka da suke yawan addabar mutanen nahiyyar afrika da suke gabar sahara.
wannan sabon maganin da likitocin kasar ingila suka samar ya bayyana cewa bawa yara kanana wannan maganin zai taimaka wajan rage mutuwar da ake samu sanadiyyar wannan cutar ta Maleria.