Akwai masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki sama dubu tara

0 49

Kungiyar masu dauke da larurar cuta mai karya garkuwar jiki ta kasa reshen jihar Jigawa ta ce ya zuwa yanzu kungiyar tana kula da lafiyar masu dauke da cutar sama dubu 9 a asibitoci daban-daban a jiharnan.

Jami’in kungiyar na jiha, Comrade Abubakar Abdullahi ne ya bayyana haka ta cikin wani shirin Radio Jigawa.

Ya ce kungiyar tana da rassa guda 9 a wasu kananan hukumomin domin inganta ayyukan kungiyar yadda ya kamata.

A jawabinta, shugabar mata ta kungiyar, Hajiya Basira Yahaya Babura ta ce kungiyar tana shiga lungu da sako na jiharnan domin wayar da kan mata da matasa masu dauke da larurar hanyoyin da zasu bi wajen kula da lafiyarsu domin kaucewa yaduwar cutar a cikin al’umma.

Basira Yahaya ta kara da cewa kungiyar tana bin matakan da suka dace domin shigar da wadanda basa cikin kungiyar ta hanyar basu takardun shaida da kuma wayar musu da kai a kafar sadarwa ta zamani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: