Karamar Hukumar Guri ta bada kwangilar kusan naira miliyan ashirin da biyar domin aiwatar da ayyukan kasa.

Shugaban Karamar Hukumar, Musa Shuaibu Muhammad Guri, ya sanar da hakan ga manema labarai.

Yace ayyukan da aka bayar sun hadar da gina rukunin gidajen ungozoma a garuruwan Takazza da kuma Madamuwa akan kudi naira miliyan biyar biyar kowannensu da gina rumfunan kasuwa a garuruwan Guri da Kadira kan kudi naira miliyan 8.

Musa Shuaibu ya kara da cewar sauran aiyukan da aka bayar kwangila sun hadar da cike wurin da za a gina kasuwar Guri kan kudi miliyan 4 da dubu 900 da gyaran masalacin Izala na garin Lafia kan kudi naira miliyan 1 da dubu 700.

Ya ce an bayar da ayyukan ne ga ‘yan jam’iyya domin raya kasa da kuma inganta tattalin arzikin ‘yan jami’yya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: