Ambaliyar ruwa ta shafe garuruwa da dama na kananan hukumomi 20 da suke Jihar Bauchi tare da hallaka mutane 22

0 81

Ambaliyar Ruwa ta shafe garuruwa da dama na kananan hukumomi 20 da suke Jihar Bauchi, tare da hallaka mutane 22 duk cikin wannan shekara.

Shugaban Sashen Ayyuka na Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Bauchi Dr Abubakar Gabarin, shine ya bayyana hakan, a lokacin da yake zantawa da Manema Labarai, inda ya ce kimanin mutane 26 ne suka ji raunika a fadin jihar sakamakon ambaliyar.

A cewarsa, annobar ta lalata amfanin gona wanda darajar kudin su ta kai Naira Biliyan 1 da Miliyan 500, wanda suka kunshi Shinkafa, Masara, Alkama, Gero da sauran kayan da ake nomawa duk cikin kananan hukumomi 20 da suke Jihar.

Shugaban Sashen, ya ce kimanin mutane dubu 25,000 ne ambaliyar ta shafa, tare da lalata Gidaje dubu 32,000, inda ya kara da cewa hukumar tana cigaba da karbar rahotanni.

Sai dai wata Majiya ta fadawa manema labarai cewa kimanin mutane 22 ne suka mutu a sanadiyar ambaliyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: