Kimanin mutune uku ne aka kashe tare da raunata wasu sakamakon wasu hare-hare a Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf

0 130

Kimanin mutune uku ne aka kashe tare da raunata wasu sakamakon wasu hare-hare da aka kai a Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a ƙauyukan Machun da Manuka, biyo bayan kashe mutane biyar da aka yi a farkon watan Agusta a yankin.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Mista Samuel Aruwan ya tabbatar da kai harin cikin wata sanarwa, yana mai cewa maharan sun shiga garuruwan ne suna harbe-harbe a kan mai tsautsayi.

Aruwan ya ce jami’an tsaro sun amsa kiran gaggawa daga garin Machun, inda da isarsu wurin suka jiyo ƙarar harbi a ƙauyen Manuka mai maƙotaka da garin.

Sai dai ya ce gawar mutane uku ‘yan sandan suka tarar da kuma adadi mai yawa na waɗanda aka raunata bayan isarsu yayin da Maharan suka tsere kafin su ƙarasa.

Kazalika, ya ce Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya samu damuwa dangane da kaiwa harin, inda ya yi addu’a ga Mamatan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: