Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani Yaro dan shekara 15 a karamar hukumar Gaya

0 87

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani Yaro dan shekara 15 mai Suna Halifa Abdulmumini a kyauyen Dutsu na karamar hukumar Gaya ta Jihar.

Kakakin Hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, shine ya tabbatar da hakan, cikin wata sanarwa da aka rabawa manema Labarai a Kano.

A cewarsa, Ofishin Hukumar ya samu kirar gaggawa kan cewa wani Yaro na fada cikin Kogi da misalin karfe 1:42 na Rana.

Kakakin ya ce bayan samun kiran ne, Jami’an su suka Isa wurin da misalin karfe 2:10, sai dai kuma tuni rai yayi halinsa, domin lokacin da suka dauko Yaron bashi da rai.

Sanarwar ta ce Jami’an hukumar sun mika gawar yaron ga Bulaman kyauyen Dutsu domin yi masa Jana’iza.

Kazalika, ya ce suna cigaba da bincike domin gano musabbabin abinda ya sa yaron ya fada cikin Kogin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: