Mutum 19 ne aka kashe a Jamhuriyar Demokradiyar Congo wanda ake zaton masu ikirarin Jahadi ne suka kai harin

0 70

A kalla mutane 19 ne aka kashe a Jamhuriyar Demokradiyar Congo, wanda ake kyautata zaton masu ikirarin Jahadi ne suka kai harin, a cewar gwamnatin Kasar.

Wani shugaban yankin da Lamarin ya faru, Mista Kakule Kalunga ya ce gawarwaki 14 ne aka tsinta.

Haka kuma ya ce Ma’aikatan kungiyar bada agajin gaggawa ta Red Cross sun shiga Dazuka domin neman sauran gawarwakin mutanen da suka mutu, biyo bayan harin da aka kaiwa kyauyen Kasanzi wanda yake kan Iyakar Beni.

Yankin da aka kai harin yana fama da hare-haren masu zafin kishin Isilama, wurin da shugaban Kasar Felix Tshisekedi, ya ke girke Jami’an tsaro.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Sabuwar Kungiyar Kare Hakkin Fararen Hula ta Rwenzori, Mista Meleki Mulala ya fitar ya bayyana cewa an kai harin ne saboda karancin Sojoji a yankin Beni.

Yan Jaridu sun tuntubi shugaban rundunar Sojin da suka yi sansani a yankin, amma bai ce komai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: