Kungiyar Daliban Jihar Yobe ta Kasa ta bayyana damuwar ta bisa kin biyan tallafin tsawon shekara 3

0 76

Kungiyar Daliban Jihar Yobe ta Kasa, ta bayyana damuwar ta bisa yadda gwamnatin Jihar taki bada tallafin karatu ga Daliban tsawon shekaru 3 kenan da suka gabata.

Shugaban Kungiyar na Kasa, Comrade Jalo Kyari, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, da aka rabawa manema madadin Daliban Jihar.

Sanarwar ta fito ne, biyo bayan zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar wanda Gwamna Mai Mala Buni ya jagoranta, inda ta amince da kashe Biliyan 7 wanjen aiwatar da ayyukan raya kasa a Jihar ba tare da tunawa da bukatun daliban ba.

Shugaban Kungiyar ya ce duk da cewa Majalisar zartarwa a baya ta amince a biya kudaden tallafin Daliban da suke karatu a Makarantun gaba da Sikandire, amma har yanzu babu abinda aka aiwatar.

Comrade Jalo Kyari, ya ce a shekarar 2020 ne, aka umarci Daliban su sayi Form din neman tallafin akan Naira 500 amma bayan sun cike Form din tare da mayarwa hukumar kawo yanzu babu abinda aka cimma.

Kazalika, ya bukaci Gwamnatin Jihar ta yi abinda ya kamata ta hanyar bada tallafin karatun ga Daliban domin rage musu radadin da suke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: