Kasar India ta yiwa mutane Miliyan 10 rigakafin cutar Corona a rana guda

0 50

Kasar India ta yiwa mutane Miliyan 10 rigakafin cutar Corona a rana guda, wanda hakan shine farko a tarihin kasar, a cewar rahoton da gwamnati ta fitar.

Ma’aikatar Lafiya ta ce kimanin mutane Miliyan 10 aka yiwa rigakafin a ranar Juma’a, fiye da mutane Miliyan 9 da dubu 200 da aka yiwa na tsawon kwanaki a baya.

An sha kalubalantar gwamnatin Jihar bisa yadda cutar Corona ta kashe mutane dubu 200,000 a tsakanin watan Afrilu zuwa Mayu na wannan shekara.

Firaminista Narendra Modi, ya bayyana farin cikinsa kan rigakafin da aka aiwatar a kasar mai mutane Biliyan 1 da Miliyan 300.

Gwamnatin Kasar ta yi Alkawarin yiwa mutane Biliyan 1 da Miliyan 100 rigakafin kafin karshen wannan shekara, sai dai shirin aiwatar da hakan yana gamuwa da tasgaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: