INEC ta bayyana cewa zata kirkira sabbin akwatunan Zabe 770 a jihar Gombe

0 80

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta bayyana cewa zata kirkira sabbin Akwatunan Zabe 770 a fadin Jihar Gombe.

Wannan kirkirar sabbin akwatunan zaben na zuwa ne bayan Jihar ta kwashe shekaru 25 da kirkira.

Shugaban Ofishin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, na Jihar Gombe Ibrahim Umar, shine ya bayyana hakan, inda ya ce karin sabbin runfunan zaben zai rage cunkoso a lokacin zabe.

Malam Ibrahim Umar, ya ce bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taron masu ruwa da tsaki kan rijistar zaben.

Haka kuma ya ce sabbin runfunar zaben 770 zasu tallafawa Al’ummar jihar, inda ya ce kawo yanzu adadin runfunar zaben Jihar ya kai dubu 2,988, biyo bayan kirkirar sabbin.

Kazalika, ya ce tun bayan da aka kirkiri Jihar Gombe shekaru 25 da suka wuce, hukumar take neman karin runfunar zaben amma abin ya ci tura.

Leave a Reply

%d bloggers like this: