NCDC ta ce an samu karin mutum 618 da suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar Najeriya

0 134

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Kasa NCDC, ta ce an samu karin mutum 618 da suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a jiya Juma’a.

NCDC ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin ta na Facebook.

A cewarta Jihar Lagos (312), Akwa Ibom (89), Edo (71), Rivers (47), Ekiti (20), Plateau (20), and Delta (15).

Sauran jahohin sune Kwara (13), FCT (11), Osun (8), Oyo (4), Ogun (3), Benue (3), Gombe (1) sai kuma Kaduna (1).

Cibiyar ta ce anyi nasarar sallamar mutane 189, bayan sun warke daga cutar, haka kuma tayi nasarar hallaka mutane 10 a jiyan.

Kawo yanzu, adadin mutanen da suka kamu da cutar a faɗin ƙasar sun kai dubu 190,333, sai dai kuma mutane dubu 169,815 sun warke.

Kazalika, adadin mutanen da cutar ta hallaka sun kai mutane dubu 2,308.

Leave a Reply

%d bloggers like this: