Gwamna Ganduje ya ce kimanin daurarru 3717 ne gwamnatin sa ta saki saboda rage cunkoso

0 93

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce kimanin Daurarru dubu 3,717 ne gwamnatin sa ta saki a fadin Jihar a wani Mataki na rage cunkoso a gidajen gyaran halayya.

A kwanakin baya, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci gwamnoni su rage cunkoso a gidajen gyaran halayya da suke kasar nan.

Gwamnan ya bayyana hakan a lokacin da Kwamatin Shugaban Kasa Kan Yiwa Fursunoni Afuwa domin rage cunkoso karkashin Jagorancin Mai Shari’a Ishaq Bello, suka kawo masa ziyara a Ofishinsa.

Gwamnan ya ce tun daga shekarar 2015 zuwa yanzu kimanin daurarru dubu 3,717 ne gwamnatinsa ta saki.

A jawabinsa, Shugaban Kwamatin Mai Shari’a Ishaq Bello, ya yabawa gwamnatin Gwamna Ganduje bisa yadda take kokarin tallafawa Shari’a domin samun Adalci.

Kazalika, ya ce kwamatinsa ya saki Fursononi 28 da suke jihar, bayan ya yi Nazari kan Laifukan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: