Gwamnatin tarayya zata raba Naira Biliyan 8 da Miliyan 800 ga mutane dubu 144,000 a Jihar Katsina

0 123

Gwamnatin tarayya zata raba Naira Biliyan 8 da Miliyan 800 ga mutane dubu 144,000 a Jihar Katsina ta cikin shirin ta na Yaki da Talauci.

Shugaban Shirin na Jihar Katsina Malam Shafi’u Abdullahi, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a jiya.

A cewarsa, za’a raba kudaden ne ta rukunin farko da na biyu, inda ya ce kimanin shekara 1 kenan da gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin a fadin jihar domin ta samu damar tantance mutanen da suka cancanta suci gajiyar shirin.

Jami’in Shirin ya ce kimanin kananan hukumomi 12 ne cikin 34 da suke Jihar suka fara cin gajiyar shirin.

Haka kuma ya ce ana cigaba da yin kokari wajen ganin sauran kananan hukumomi 22 da suke Jihar sun ci gajiyar shirin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa an fara raba kudaden ne, a kananan hukumomin Batagarawa, Daura, Ingawa da kuma Bindawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: