Maleria ta kashe mutane 67 cikin watanni 3 a karamar hukumar Hadejia

0 81

Kimanin mutane 67 ne zazzabin cizon sauro ya yi Ajalinsu a karamar hukumar Hadejia cikin watanni 3 na farkon wannan shekara.

Haka kuma kimanin mutane dubu 15,059 ne suka harbu da zazzabin cizon sauro cikin watannin a fadin karamar hukumar ta Hadejia.

Shugaban Sashen Ruwa da Tsaftar Muhalli na Karamar hukumar Alhaji Muhammad Abdullahi, shine ya sanar da hakan a lokacin da shugaban Majalisar karamar hukumar Hon Abdulkadir Bala Umar T.O, ya kaddamar da aikin feshin sauro a Hadejia.

A cewarsa, rahoton da sashen ya tattara daga cibiyoyin Lafiya da suke karamar hukumar, ya yi nuni da cewa cikin watanni 3 na farkon shekarar nan, Mutane 11,505 ne suka harbu da zazzabin cizon sauro, sai kuma Yara 1,599 da suka gamu da zazzabin.

Shugaban Sashen ya ce Mata masu Juna biyu 1,955 ne suka harbu da zazzabin a yayin da 16 daga cikin su suka mutu a sanadiyar cutar duk cikin watanni 3 na farkon shekarar nan.

Kazalika, ya ce Majalisar Karamar hukumar ta samar da maganin feshi katan 10, da Safar hannu 55 da Injin feshi 55, da Takunkumin fuska 150 da kuma Madara gwangwani 180 yin fara aikin feshin a Mazabu 11 da suke yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: