Gwamnatin jihar Sokoto ta karbi Naira Biliyan 2 da Miliyan 500 a matsayin gudunmawar mai kamfanin BUA

0 117

Gwamnatin Jihar Sokoto ta karbi Naira Biliyan 2 da Miliyan 500 a matsayin gudunmawar Gidauniyar Alhaji Abdulsamad Rabiu domin gina Tsangayar Ilimin Likitanci a Jami’ar Jihar.

Kakakin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Muhammad Bello, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a Sokoto.

A cewarsa, Tsohon Ministan Lafiya na Kasa, Dr Aliyu Hong, shine ya mika gudunmawar a madadin Shugaban Gidauniyar.

Sanarwar ta ce za’ayi amfani da wasu kudaden domin ginin Sashen Mulki a Kwalagen Lafiya ta Sultan Abdurrahman dake Gwadabawa.

Haka kuma ya ce wasu kudaden za’ayi amfani da dasu wajen ginin Sashen Mulki, da Dakin Karatu, da kuma Asibiti, a Kwalegin Koyan Aikin Jinya ta Tambuwal.

Kazalika, Sanarwar ta ce Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ya umarci Ma’aikatar Kasafi ta fara shirye-shiryen kwarya-kwaryan Kasafin kudaden kan yadda za’a kashe kudaden.

Leave a Reply

%d bloggers like this: