Gwamnatin jihar Jigawa zata gina manyan makarantu 5 a masarautu 5 da suke fadin Jihar nan akan kudi Naira Biliyan 2

0 124

A wani Mataki na Rage Cunkoson Dalibai a Makarantu, Gwamnatin Jihar Jigawa zata gina Manyan Makarantu 5 a Masarautu 5 da suke fadin Jihar nan akan kudi Naira Biliyan 2.

Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta Jihar Jigawa Dr Lawan Yunusa Danzomo, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake jagorantar Mambobin Kwamatin Kungiyar Editoci ta Kasa wanda suke duba ayyukan raya kasa a Jigawa.

A cewarsa, gwamnatin Jiha ta dauki matakan ne, a wani yunkuri na rage cunkoson Dalibai a fadin Jihar nan, musamman a Makarantun Sikandire, inda ya kara da cewa hakan zai rage fargabar tsaro da Iyayen Dalibai suke da ita.

Dr Lawan Yunusa Danzomo, ya ce kowacce Makaranta 1 da za’a gina a Masarautu 5 din da suke Jihar nan, za’a kashe Mata Naira Miliyan 423, inda ya ce aikin ginin Makarantun a Masarautun Dutse da Kazaure ya kai kaso 80 cikin 100.

Kwamishinan, ya ce a kwanan nan ne za’a fara aikin ginin a Masarautun Gumel da Hadejia da kuma Ringim.

Kazalika, Kwamishinan, ya ce Makarantun zasu rika samarda Ilimin Kimiyya da Fasaha da kuma Kasuwanci, inda ya kara da cewa gwamnatin Jiha zata samar da Kwararrun Malamai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: