Gwamna Badaru Abubakar ya yiwa daurarru 79 da suke gidan gyaran halayya afuwa

0 65

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar, na Jihar Jigawa ya yiwa daurarru 79 da suke Gidan Gyaran Halayya Afuwa, a wani yunkuri na bikin cikar shekaru 30 da kirkirar Jihar Jigawa.

Kakakin Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Halayya ta Jihar Jigawa SC Mohammed Sani, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse.

A cewarsa, Babban Lauyan Gwamnati, kuma Kwamishinan Shari’a Dr Musa Adamu Aliyu ya bukaci wadanda aka yiwa afuwar su kasance masu nuna hali nagari.

Sanarwar ta ce Daurarru 79 da aka saki sun fito ne daga gidajen halayya na Dutse, Kazaure, Kiyawa, Birninkudu, Gumel, Hadejia, Jahun, Gwaram, Garki, Babura da Ringim, da kuma Makarantar gyaran halayyar Yara ta Kafin Hausa.

Da yake Jawabi, Kwamfuturolan Hukumar na Jihar Jigawa Malam Mu’azu Garba, ya godewa Gwamna Badaru bisa sakin Fursunonin.

Haka kuma ya ce hukumar zata yi aiki tukuru domin tabbatar da cewa daurarrun da suke gidan sun sami horo kan Sana’oin hannu kafin su koma cikin Al’umma.

Kazalika, Sanarwar ta ce kowanne daga cikin Fursunonin da aka saka an basu kudaden Mota domin komawa gidan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: