Rundunar Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da sace mutane 4 a karamar hukumar Sabon Gari

0 86

Rundunar Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da sace mutane 4 a yankin Zangon Shanu na Unguwar Liman ta karamar hukumar Sabon Gari ta Masarautar Zazzau.

Kakakin rundunar ASP Muhammed Jalige, shine ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN.

A cewarsa, mutanen da aka sace sun kunshi Maza 3 da Mace 1.

Haka kuma ya ce tuni aka tura rundunar da take yaki da Masu satar mutane, domin farautar yan bindigar.

ASP Muhammad Jalige, ya bukaci mutane su rika bawa Jami’an tsaro bayanan sirri ta yadda zasu dakile hare-haren masu Garkuwa da mutanen domin neman kudin fansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: