Hukumar gyaran hanyoyin mota ta kasa ta bada kwangilar gina gada a wani bangare na hanyar motar Hadejia zuwa Gamayin da ambaliyar ruwa ta lalata.
A jawabinsa wajen kaddamar da aikin a kauyen Wailare, jami’in shiyya na hukumar Injiniya Hussaini Abubakar yace an bada kwangilar ne ga kamfanin Dan Adida, kuma ana san kammalawa cikin watanni biyu masu zuwa.
- ’Yan Sanda Sun Kwato Miyagun Kwayoyi 5,916, Sun Kama Dillalai 7 A Jigawa
- ’Yan Sanda Sun Kwato Wayoyi 41 da Kwayoyi da Ake Zargin Sun Kai Naira Miliyan 6.5 A Borno
- Diphtheria: Adadin Waɗanda Suka Mutu Ya Karu Zuwa 27 A Plateau
- Yadda Aka Yi Wa Mai Sharhi A Kafafen Sada Zumunta Kisan Gilla A Kano
- Wani Mutum Ya Shiga Hannu Kan Zargin Kashe Mahaifiyarsa A Osun
Yace Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ne ya samo aikin bisa la’akari da muhimmancinsa ga tattalin arzikin jihohin Jigawa da Bauchi da Yobe da kuma Borno.

A sakonsa zuwa wajen bikin kaddamarwar, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, ta bakin mai bashi shawara na musamman akan ilimin gaba da sakandire, Muhammad T. Muhammad, yace bayar da kwangilar zai dafawa kokarin gwamnatin jihar na gyaran titunan da ambaliyar ruwa ta lalata a fadin jihar.