Majalisar zartarwar jihar jigawa ta amince da kudi naira miliyan 330 domin samar da fitilun kan titi masu amfani da hasken rana a garuruwan Hadejia da Chai-Chai da Zandam da kuma Babura.

Kwamishinan yada labarai, matasa da wasanni, Bala Ibrahim Mamsa, ya sanar da hakan jim kadan bayan kammala taron majalissar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse.

Yace an bada kwangilar samar da fitilun kan titi masu amfani da hasken rana a garin Babura ga kamfanin Aren kan kudi naira miliyan 138, wanda za a kammala cikin watanni 3.

Majalisar ta kuma amince da bayar da kwangilar samar da fitilun kan titi masu amfani da hasken rana a nan Hadejia akan kudi naira miliyan 90, wanda ake sa ran kammalawa cikin watanni uku.

Ya kuma bayyana cewa an bayar da wani aikin samar da fitilun kan titi masu amfani da hasken rana a garin Chai-Chai na karamar hukumar Dutse da Zandam na Karamar Hukumar Gwaram.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: