Kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC ta bayyana gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar a matsayin dan kishin kasa tare da hangen nesa da jagoranci nagari da jajircewa wajen ganin Najeriya ta kasance dunkulalliyar kasa mai wadata.

Gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC, Abubakar Atiku Bagudu, ya bayar da wannan yabo a sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwar Gwamna Muhammad Badaru Abubakar bisa cikarsa shekaru 59 a duniya.

Kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC ta kara da cewa gwamnan ya kasance mai kwazo da son kai wajen samar da ingantattun bayanai masu gamsarwa ga hanyoyin gudanar da mulki a jihar Jigawa da ma na ƙasa baki ɗaya.

Gwamna Bagudu ya ce gwamnonin APC za su cigaba da aiwatar da shirye-shiryen da ke karfafa karfin jihohin su don samar da ayyukan yi, da karfafa ayyukan tattalin arziki, da rage rashin daidaito da talauci a Najeriya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: