‘Yan bindiga sun kashe mutum 20 tare da garkuwa da wasu da dama Sanon Birni na jihar Sokoto

0 84

‘Yan bindiga a daren jiya sun kashe akalla mutane 20, tare da yin garkuwa da wasu da dama a Gatawa, wani kauye a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Ana kallon kauyen na manoma a matsayin daya daga cikin kauyukan da ke da tsaro a gabashin jihar, inda ‘yan ta’adda suka yi ta kai hare-hare.

Mummunan harin ya zo ne sa’o’i 24 bayan wani a Gangara, cikin wannan karamar hukumar.

Wani mazaunin yankin mai suna Bashir Gobir, ya ce kanwarsa na cikin wadanda aka sace.

Bashir Gobir ya ce bai san adadin mutanen da aka kashe a harin ba.

Da aka tuntubi mai magana da yawun ‘yan sanda a Sakkwato, Sanusi Abubakar, ya ce yana halartar wani taro kuma ya yi alkawarin zai biyo kiran.

Leave a Reply

%d bloggers like this: