NCDC ta ce kimanin sabbin mutane 295 ne suka harbu da cutar Corona a kasar nan

0 150

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta ce kimanin sabbin mutane 295 ne suka harbu da cutar Corona a kasar nan baki daya.

Cibiyar ta NCDC ta ce mutanen da suka kamu da cutar sun fito ne daga jihohi 19 da suke kasar nan ciki harda babban birnin tarayya Abuja.

A wannan karon birnin Abuja ne yake da kaso 81, sai Gombe 43 da Osun 32.

Sauran Jihohin sune Kaduna (25), Rivers (20), Delta (17), Edo (14), Ogun (11), Oyo (9), Plateau (9), Akwa Ibom (7), Bayelsa (7), Zamfara (6), Kano (4), Ondo (3), Abia (2), Nasarawa (2), Benue (1), Ekiti (1), and Niger (1).

Cibiyar ta ce mutane 317 ne aka sallama daga cibiyoyinta da suke fadin kasar nan, bayan sun warke daga cutar.

Haka kuma an bayar da rahoton cewa mutane 6 ne cutar ta hallaka a jiya, wanda hakan ne ya kawo adadin mutanen da cutar ta hallaka a kasar nan zuwa dubu 2,695.

Kawo yanzu kimanin mutane dubu 205,047 ne suka harbu da cutar a kasar nan baki daya tun bayan bayyanarta, haka kuma an samu mutane dubu 193,260 da suka warke daga cutar baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: