An Dakile Yunkurin Juyin Mulki da Wasu Jami’an Soji Suka Kitsa A Nijeriya

0 135

Rahotanni daga hukumomin tsaro a Nijeriya sun bayyana cewa, an gano tare da dakile wani yunkurin juyin mulki da ake zargin wasu jami’an soji suka shirya, wanda aka ce an tsara shi ne domin a aiwatar a ranar 25 ga Oktoba, 2025.

Masu bincike sun ce mafi yawan wadanda ake zargi ‘yan Arewa ne, sai dai daya daga cikinsu, Kyaftin Yusuf, wanda ya fito daga Jihar Osun, yayin da ake zargin shirin ya kunshi kashe Shugaban kasa, Mataimakinsa Kashim Shettima, ministoci, shugabannin sojoji da sauran manyan jami’an gwamnati.

Rahoton ya nuna cewa hukumomin tsaro sun gano wata hadaddiyar kungiya mai karfi da kudi, wadda ta kunshi jami’an Soja, Ruwa da na Sama, da ake zargin sun hada kai domin rushe kundin tsarin mulki da kwace iko.

Masu binciken sun ce an raba kudi tsakanin naira miliyan biyu zuwa biyar ga wasu muhimman ‘yan shirin, inda aka yi amfani da manhajojin sadarwa masu boye sakonni domin tsara tafiyar da shirin.

Rahoton ya kara da cewa an gano wata hanyar bin diddigin kudade da ake zargin wani Kanar ya raba domin shirya dabaru da yuwuwar tayar da hankali, yayin da Hukumar Leken Asirin Kudi ta Nijeriya ke nazarin sahihan bayanan kudin.

Daya daga cikin wadanda ake zargi, Laftanar Kanar Bappah, ya zama shaida, inda rahoton ya ce yana ba da cikakken hadin kai bayan ya amincewa da rawar da ya taka tare da bayyana hanyoyin daukar mutane, kudade da sadarwa.

Hukumomin tsaro sun ce barazanar ta kasance babba saboda hadin gwiwar sassan soji daban-daban, da kuma shigar manyan jami’ai har zuwa mukamin Birgediya Janar, lamarin da ya sa aka dauki matakan gaggawa domin kare zaman lafiyar kasa.

Leave a Reply