Kwankwaso Ya Ce Abba Kabir Yusuf Zai Yi Danasanin Sauya Sheƙa Zuwa APC

0 372

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf da mambobin gwamnatinsa za su yi dana sanin matakin da suka ɗauka na sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa da safiyar Laraba, Kwankwaso ya bayyana cewa sauya shekar gwamnan ya ba mutane da dama mamaki, yana mai cewa har yanzu ya gaza fahimtar dalilin barin NNPP zuwa APC.

Kwankwaso ya ce wasu na ganin cewa sauya shekar an shirya ta ne tun da fari a tsakaninsu, amma ya musanta hakan, yana mai cewa abin da ke faruwa yana masa kama da mafarki.

 Gwamna Abba Yusuf ya sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar Juma’a, sannan ya shiga jam’iyyar APC a hukumance ranar Litinin, inda aka yi masa tarba ta musamman a gidan gwamnati tare da manyan shugabannin APC a Kano.

Sauya shekar ta faru ne kasa da shekaru uku bayan zaben Abba Yusuf a ƙarƙashin tutar NNPP, inda gwamnan ya ce komawarsa APC na da nasaba da bukatar yin aiki kafada da kafada da gwamnatin tarayya domin ci gaban jihar.

 Sai dai Kwankwaso ya ce abin takaici ne ganin yadda gwamnan ya mika amanar da jama’ar Kano suka bawa NNPP zuwa APC.

Leave a Reply