Kotun Jigawa Ta Saki Ja’o Sabo, Ta Umarci A Biya Shi Diyyar Naira Miliyan 10 Bayan Tsare Shi Shekaru Goma Ba Tare da Shari’a Ba
Babbar Kotun Jihar Jigawa ta bayar da umarnin sakin Ja’o Sabo nan take, wanda aka tsare fiye da shekaru goma ba tare da gurfanar da shi gaban kotu ba, tare da ba shi diyyar naira miliyan goma.
Kotun ta kuma umarci hukumomi da su nemi afuwar Sabo a bainar jama’a, inda za a watsa neman afuwar ta kafafen rediyo a faɗin Jihar Jigawa.
Rahotanni sun nuna cewa an kama Sabo ne tun a shekarar 2014 bisa zargin haɗin baki da fashi da makami, amma shari’arsa ba ta kai matakin shari’a ba na tsawon shekaru goma.
Yayin yanke hukuncin a Birnin Kudu ranar Talata, Mai Shari’a Ado Yusif Birnin-Kudu ya ce tsare Sabo na dogon lokaci ya zama take haƙƙoƙinsa na kundin tsarin mulki.
Alkalin ya umarci Gwamnatin Jihar Jigawa, Antoni Janar na jihar da kuma Kwamishinan ’Yan Sanda dasu biya Sabo naira miliyan goma a matsayin diyya kan tsare shi ba bisa ƙa’ida ba.
Kotun ta ce tsarewar ta karya sashe na 35, 36, 41 da 46 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa gyara, tare da wasu tanade-tanaden Kundin Yarjejeniyar Afirka kan ’Yancin Dan Adam.
Lauyan Sabo, Baffa Al’asan, ya ce hukuncin ya nuna rawar da kotuna ke takawa wajen kare ’yancin jama’a da tabbatar da bin doka da oda.