An gano matattun dake karbar Fansho sama da 300 a Bauchi

0 177

Akalla mamata dari uku da goma sha biyu aka samu cikin yan fanshon kananan hukumomi, wadanda ake biya fansho a jihar Bauchi.

Kazalika, an gano mamata tara da ake biya fansho a gwamnatin jihar.

Mai bawa gwamnan Bauchi shawara ta musamman kan harkokin aikin gwamnati, Abdon Gin, wanda ya sanar da haka a wajen taron manema labarai jiya a Bauchi, yace Gwamnatin jihar ta adana kudi sama da naira miliyan casa’in da daya da dubu dari hudu da hudu, da dari biyu da casa’in da shida da kwabo goma sha tara bayan gano mamatan.

Yace wani kwamitine da gwamnan jihar ya kafa domin tantance ma’aikata da basu da shaidar banki, ya bankado badakalar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: