

Wasu alkaluma da babban bankin kasa CBN ya fitar na nuni da cewa, asusun kasar wajen Najariya ya fado da kimanin dalar Amurka miliyan 544, daga jimillar dala biliyan 36 da miliyan 17 a 1 ga watan yuli, zuwa jimillar dala biliyan 35 da miliyan 62 a ranar 13 ga watan Agustan da muke ciki.
A wani zama da kwamatin tsare tsaren kudade ya gudanar, babban bankin ya nanata cewa, faduwar farashin mai ya shafi harkokin musayar kudaden kasarnan.
- Abubuwa 5 da suka zama wajibi lokacin sanyi
- An ƙaddamar da kudin kariya ga ƴan jarida da masu fafutukar ƴancin amfani da yanar gizo
- Yadda ake duba suna don zama ma’aikacin damara na 2020 a Nijeria
- Me Ƙungiyar Izala ta ce kan matsalolin tsaro a Najeriya?
- Muhimmiyar shawara ga manoma kan Noman rani
A cewar kwamatin tsare tsaren, matakan kulle da na tsagaita tafiye tafiye, da aka sanya sabida Corona, zai cigaba da yin tasiri wajen nukusa tattalin arzikin kasarnan.
A zaman karshe da kwamatin yayi, gwamnan babban bankin Mr Godwin Emefiele, ya bukaci gwamnati da ta dauki matakan rage dogaro da mai, ta hanyar fadada harkokin tattalin arziki da tattara kudaden haraji.