Kusan Mutane 2000 sun rabauta da Tallafin Gwamnatin Tarayya na 5000 a Birniwa

0 79

Kimanin Masu karamin karfi dubu daya da dari biyar da talatin da hudu ne da aka zabo daga garuruwa goma sha biyar a yankin karamar hukumar Birniwa zasu amfana da tallafin naira dubu biyar-biyar karkashin shirin rage radadin talauci na kasa.

Manajan ofishin shirin biyan kudade na jiha, Kabiru Yahaya Abdulkadir, ya bayyana haka lokacin raba koren katin karbar tallafin a sakatariyar karamar hukumar Birniwa.

A nasa jawabin shugaban karamar hukumar wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Alhaji Umar Baffa ya yabawa gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari bisa bada tallafi ga masu karamin karfi.

Tunda farko a jawabinsa jami’in kula da shirin na karamar hukumar, Shehu Baba Birniwa ya ce wannan shi ne karon farko da al’ummar karamar hukumar zasu ci gajiyar shirin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: