An jinkirta buɗe makarantu a zangon farko da aka tsara farawa a yau a Zambia

0 127

Mahukunta a Zambiya sun jinkirta buɗe makarantu a zangon farko da aka tsara farawa a yau zuwa nan da makonni uku masu zuwa.

Wannan ya zo ne bayan ƙaruwar mace-mace da ke da alaƙa da ɓarkewar cutar kwalara a ƙasar.

An dakatar da buɗe makarantun firamare da na sakandare har sai 29 ga watan Junairu, a matsayin matakin shawo kan ɓarkewar cutar mai hatsari.

An samu rahoton mutuwar mutum sama da 200 a ƙasar tun Oktoban bara dake da alaka da cutar.

Cikin sa’a 24 da ta gabata, an samu mutuwar mutum 27 ta dalilin cutar a Zambiya sai mutum 26 a Lusaka, babban birnin ƙasar sannan mutum guda a Kabwe da ke maƙwabtaka da birnin.

Mahukuntan lafiya sun ce akwai ɓuƙatar a gaggauta ɗaukar mataki da kuma faɗakarwa kan cutar.

Tun Oktoban da ya gabata, an samu rahoton sama da mutum dubu 5 da suka kamu da cutar. Shugaban ƙasar Hakainde Hichilema, ya ce ya taƙaita hutunsa domin zama kan gaba wajen jagorantar yaƙi da ɓarkewar cutar. A cewar hukumar kula da yaɗuwar cututtuka ta CDC, Zambiya na cikin ƙasashe 18 a duniya da ke fama da ɓarkewar kwalara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: