An kama mutane 19 bisa zargin su da aikata laifukan fashi da makami a jihar Bauchi

0 72

Rundunar Yan Sandan Jihar Bauchi ta ce tayi nasarar kama mutane 19 bisa zargin su da aikata laifukan fashi da makami, kisa da kuma Garkuwa da mutane a jihar.

Kakakin Rundunar Yan sandan Jihar ASP Ahmed Wakil shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya.

A cewarsa rundunar ta kama Idi Abdullahi, Rabiu Sulaiman, Aliyu Malam alias Majo and Hassan Bako bisa zargin su da kashe Jibril Aliyu ta hanyar harbin sa gidan sa.

Haka kuma ya ce mutanen sune suka je gidan Ibrahim Dai tare da sa ce Dan sa mai suna Idi Jibrin, inda suka bukaci Naira Miliyan 1 da dubu 500 a matsayin kudin fansa kafin sakin sa.

Sanarwar ta ce rundunar kuma tayi nasarar kama Nasir Gaddafi, da Abdulrahman Mahmood da kuma Kabiru Saleh bisa zargin su da yiwa wani Alhaji Dan’asabe Bayara a gidan sa, tare da kashe wani mai suna Danjuma Umar.

Kakakin Rundunar ya ce Kazalika, sun yi nasarar kama wani mai suna Enoch Yohanna dan shekara 27 bisa zargin sa da kashe Budurwarsa bayan ta Haifa masa Yaya 2.

Leave a Reply

%d bloggers like this: