An kashe akalla fararen hula 20 a kusa da birnin Gao da ke Arewacin Mali ranar Asabar.

Hukumomi sun zargi mayaka masu ikirarin jihadi, kuma sun ce lamarin akwai tayar da hankali sosai, lura da yadda fararen hula ke ci gaba da tserewa daga yankin saboda hare-hare.

Ko a ranar Lahadi an kashe sojan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, bayan taka nakiya a Kidal da ke arewacin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta damu da yadda rashin tsaro ke dada kamari a yankunan Gao da Menaka.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: