An kashe jami’an shige da fice guda biyu a kan iyakar Kangiwa

0 155

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba ne a ranar Litinin din da ta gabata sun kai hari tare da kashe jami’an shige da fice guda biyu a kan iyakar Kangiwa, da ke karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar shige da fice ta kasa reshen jihar Kebbi, DSI Abdullahi Isah ya fitar, ya ce ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne  sun kai farmaki kan jami’an ‘yan sanda a kofar shiga garin Gari Garba mai tazarar kilomita 12 daga garin Kangiwa wanda ya yi sanadiyar mutuwar jami’an biyu da ke bakin aiki a bakin iyaka.

Wadanda suka rasun su ne Isah Nafi’u da Garba Haruna Fana, wadanda duk an yi jana’izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Ya kara da cewa a yayin da rundunar ta ke alhinin rasuwar jami’an ‘yan sanda, an fara gudanar da bincike don gano bakin zaren wadanda suka aikata wannan danyen aikin. Ya kuma kara da cewa harin ba zai dauke hankalinsu daga ayyukansu na kula da iyakokin yadda ya kamata ba don kakkabe masu aikata laifuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: