Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Baduru Abubakar ya rantsar da sabon babban Khadin Jihar tare da karin wasu alƙalan manyan kotuna a fadar gwamnatin jihar a jiya.
Da yake magana a wurin taron da aka yi shi ba tare da cikowar jama’a ba saboda halin da ake ciki na bukatar karancin cunkoso da bayar da tazara, Gwamna Badaru bukaci sabbin masu Shari’ar da su ji tsoron Allah yayin da suke aiwatar da aikin su.

Kwamishinan Shari’a na jihar Dr. Musa Adamu Aliyu ne ya jagoranci rantsuwar sabbin alƙalan biyu da kuma babban Khadin.
- ‘Yan bindiga sun hallaka mutane 6 da kuma raunata wasu 4 a jihar Kaduna
- Lauyoyin Atiku sun shigar da kara suna kalubalantar zuwan Tinubu Jami’ar jihar Chikago
- An samu nasarar dakile wani yunkurin juyin mulki da ya nufaci hambarar da gwamnatin Kyaftin Traore
- Sama da mutane 4,000 sun si rajista da shirin auren zawarawa a Kano
- Yaƙin da ake a ƙasar Sudan zai iya yaɗuwa zuwa sauran ƙasashen Afirka – Abdel Fattah al-Burhan
Alƙalan manyan kotunan su ne mai shari’a Musa Ubale da mai shari’a Husseina Aliyu Adamu sai kuma Khadi Muhammad Sani Salihu.

Taron rantsuwa ya samu halartar mataimakin gwamna Malam Umar Namadi da kakakin majalisar dokoki ta jihar Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini.
