An sake samun takaitaccen barkewar fada tsakanin bangarori biyu da basa ga maciji da juna a birnin Tripoli na kasar Libya

0 71

An samu takaitaccen barkewar fada tsakanin bangarori biyu da basa ga maciji da juna, a Tripoli babban birnin kasar Libya.

Mambobin wani bangare na gabashin kasar sun iso birnin cikin dare a kokarinsu na kwace madafun iko. Daga nan ne suka fice daga birnin bayan shafe sa’o’i da dama ana arangama.

‘Yan rakiya dauke da makamai sun raka Fathi Bashagha, wanda majalisar dokokin kasar ta nada a matsayin firayim minista a gabashin Libya.

Ya jima yana kokarin karbar mulki daga hannun Abdulhamid al-Dbeibah, wanda aka nada a matsayin firaminista bayan tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta a bara.

A wani labarin kuma, kotun soji a kasar Tunisiya ta yanke hukuncin dauri kan wasu ‘yan majalisar dokokin kasar hudu bisa zargin cin zarafin ‘yan sanda a bara.

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Saif Eddine Maklouf, wanda ke jagorantar jam’iyyar Karama a majalisar dokokin da aka rusa.

Saif Eddine Maklouf wanda fitaccen mai sukar shugaba Kais Saied ne, an yanke masa hukuncin daurin watanni biyar a gidan yari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: